1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗe baji kolin kayayyakin fasahar ƙere-ƙere a Hannover

April 19, 2010

Sabbin samfurin naurorin ƙere-ƙere na zami fiye da 4000 aka baje kolinsu a kasuwar baje kolin Hannover ta bana a ƙasar Jamus

https://p.dw.com/p/N0SO
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a bikin baje kolin fasahar ƙere-ƙere a HannoverHoto: picture alliance/dpa

A yau ne aka buɗe bikin baje kolin kayayyakin fasaha dana ƙere-ƙere a birnin Hannover a nan Jamus. Shugabar gwamnati Angela Merkel wadda ta ƙaddamar da bikin buɗe baje kolin tace ta yi imanin zaá iya shawo kan matsalar tattalin arziki da ta addabi duniya. Merkel tare da Firaministan Italiya Silvio Berlusconi sun kewaya wasu rumfunan a wajen baje kolin. Bikin baje kolin wanda zaá shafe tsawon kwanaki biyar ana gudanarwa ya sami halartar kamfanoni kimanin 4,800 waɗanda suka baje kolin kayayyakinsu da suka haɗa da sabbin fasahar ƙere ƙere har 4000. Ƙungiyar kamfanonin ƙere-ƙere ta nan Jamus tace ta sami odar kayayyaki daga masu hulɗa da ita kuma suna sa ran zaá sami gagarumin cigaba a wannan shekarar. Kamfanin ƙera injina na Jamus shine kamfani na biyu mafi girma a ƙasar bayan kamfanonin ƙera motoci.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita      : Umaru Aliyu