1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗa taron shugabanin ƙasashen membobin Majalisar Ɗinkin Dunia

September 19, 2006
https://p.dw.com/p/Buiv

Sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan, ya gabatar da jawabin bankwana a taron shekara shekara na Majalisar da ka hada shugabanin ƙasashe da jami´an diplomatia na dunia.

A watan Desember mai zuwa, Koffi Annan zai sauka daga wannan muƙami da ya rike a tsawan shekaru 10.

A cikin jawabin da ya gabatar, sakatare jannar ya yi kira ga ƙasashen dunia su gaggauta kawo ƙarshen rikicin yankin gabas ta tsakiya.

Muddun palestinawa za su ci gaba da rayuwa cikin mamaya , tare da nuna masu azaba da ƙasƙanci, muddun yahudawa za su ci gaba da zama cikin ɗar- ɗar, na hare haren ƙunar baƙin wake,to tashe-tashen hankulla za su ci gaba da dawwama ko ina cikin dunia.

A jawabin da yayi, shugaban ƙasar Amurika Georges Bush, ya bayyana manufofin gwamnatin sa a kan al´amuran da ke wakana, a yankin gabas ta tsakiya mussamman a ƙasashen Afghanistan, Iran Libanon, Syria da Irak, da kuma rikicin Isra´ila da Palestinu.

Shugaban kasar Amurika ya yi kira ga Majaliosar Dinkin Dunia ta himmantu wajen aika dakarun shiga tsakanin ayankin Darfur na ƙasar Sudan