An buɗa taron NATO a birnin Lisabon na ƙasar Portugal
November 19, 2010Shugabannin ƙasashen ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO sun hallara a birnin Lisbon na ƙasar Portugal a taron ƙoli na ƙungiyar da aka soma a yau.
Taron wanda za a kwashe kwanaki biyu ana tattauna a ƙarshe ana sa ran shugabanin ƙasashen guda 28 za su amince da mahimman shawarwari waɗandada su ka haɗa da kawo sauye-sauye ga rundunar tsaron nan gaba a cikin shekaru masu zuwa, tare kuma da duba hanyoyin janye bradan ƙungiyar daga ƙasar Afganistan kafin ƙarshen shekara ta 2014 lokacin da za su mayar da al´amuran tsaro ga sojojin na Afganistan.
Ministan tsaro na ƙasar Jamus KARL Theodor zu Guttenberg ya shaida cewa janye sojojin Ƙungiyar daga Afganistan zai zama wata hanyar saki ga sojojin ƙungiyar:
Ya ce a ra'ayinsa, wannan wata dama ce ta kawo ƙarhen barazana da sojojinsu ke fama da ita a Afganistan kuma a ƙalla kafin nan da shekara ta 2014 za su iya cimma mafufofinsu.
Mawallafi: Abdurahman Hassane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi