An binne gawar Abu Musab al-Zarqawi, a wani gu na sirri a ƙasar Iraqi. | Labarai | DW | 02.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An binne gawar Abu Musab al-Zarqawi, a wani gu na sirri a ƙasar Iraqi.

Bisa cewar wani kakakin rundunar sojin Amirka a Iraqi, Manjo William Wilhoite, a cikin wata fira da ya yi da kamfanin dilllancin labaran AFP yau a birnin Bagadaza, Mahukuntan Iraqi sun binne gawar shugaban ƙungiyar al-Qaeda a ƙasar, Abu Musab al-Zarqawi, wanda dakarun Amirkan suka kashe ran 7 ga watan jiya, a wani harin da suka kai kan maɓuyarsa a garin Baquba da ke arewacin birnin Bagadaza. Kakakin ya ce rundunar sojin Amirkan ta miƙa gawar al-Zarqawin ne ga jami’an gwamnatin Iraqin, waɗanda kuma suka sa aka binne shi ba tare da bayyana ko ina ne a cikin ƙasar ba.

A cikin wani saƙon da aka jiyo a shafin yanar gizo ta Internet kuma, shugaban Ƙungiyar Al-Qaedan, Usama Bin Laden, ya yi ikira ga a mai da gawar al-Zarqawin zuwa ƙasarsa ta asali, wato Jordan.