An bindige wasu Faransawa a Mauritania | Labarai | DW | 24.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bindige wasu Faransawa a Mauritania

Wasu yan bindiga dadi sun kashe wasu yan yawon shakatawa faransawa guda 4 tare da raunana na biyar dinsu,ayankin gashin birnin Nouakchott,dake zama fadar gwamnatin kasar Mauritania.Babban jamiin rundunar yansandan dake garin Aleg,inda aka harbe wadannan yan yawon shakatawa ,ya bayyana cewar an yiwa faransawan fashi da bakin bindiga,kafin a hallaka su har lahira.Ofishin jakadancin kasar faransa dake kasar ta Mauritania ya tabbatar da cewar mutum na biyar din,ya samu mummunan rauni.