An bindige wani sojan Amirka a cikin daren jiya a birnin Bagadaza. | Labarai | DW | 05.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bindige wani sojan Amirka a cikin daren jiya a birnin Bagadaza.

Wani raoton da muka samu ɗazu-ɗazun nan kuma ya ce, an bindige wani sojan Amirka har lahira a birnin Bagadaza a cikin daren jiya. Kawo yanzu dai, yawan sojojin Amirkan da suka mutu a Iraqi, tun da suka afka wa ƙasar a cikin shekara ta 2003, ya tashi zuwa dubu 2 da ɗari 8 da 26, inji kamfanin diillancin labaran nan AFP, wanda ke dogaro kan alƙaluman da ma’aikatar tsaron Amirkan wato Pentagon ta buga.