An bayyana lalata da cin zarafin mata a Kongo da cewa cansa ce | Labarai | DW | 16.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bayyana lalata da cin zarafin mata a Kongo da cewa cansa ce

Wani babban jami´in MDD ya kwatanta yiwa mata fyade a JDK da cewa ta zama tamkar wata cutar cansa a cikin kasar. Shugaban hukumar ba da taimakon jin kai na MDD Jan Egeland ya fadawa kwamitin sulhu cewa sojojin kasar ta Kongo sun yiwa dubban mata fyade a fadin kasar baki daya. Egeland wanda ya kai ziyara Kongo kwana kwanan nan ya yi tir da gazawar gwamnatin wucin gadin kasar da kuma MDD ta kawo karshen aikata wadannan laifukan a ckin kasar ta Kongo. Ya ce ya fadawa shugaba Josef Kabila da ya fito fili ya yi Allah wadai da wannan cin zarafin sannan ya sallami ko kuma ya hukunta masu hannu a ciki. A ranar 29 ga watan oktoba za´a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar inda za´a yi takara tsakanin Kabila da mataimakinsa Jean-Pierre Bemba.