1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An bayyana ilimi a matsayin makamin yaki da talauci.

A gun wani taron koli da aka yiwa lakabi da taron karni da Majalisar Dinkin Duniya ta kira a cikin watan satumban shekara ta 2000, gamaiyar kasa da kasa ta dorawa kanta alhakin rage yawan masu fama da talauci a duniya zuwa rabinsu a yanzu kafin shekara ta 2015. Babban matakin yakar talauci dai shine ilimi da kuma tarbiya ta gari. To amma duk da wannan buri da aka sa gaba har yanzu ba ta canza zane ba a fannen ba da ilimi ga kowa da kowa. Domin yanzu haka a duk fadin duniya akwai mutane kimanin miliyan 900, daukacinsu mata da ba su iya rubutu da karatu ba. Sannan kuma akwai kananan yara sama da miliyan 100 da ba su taba samun wani ilimi na firamare ba, wato kenan da akwai bukatar bullo da sabbin dubaru bisa manufa. To a halin da ake ciki akwai kananan yara miliyan 130 a duk fadin duniya da ba sa zuwa makaranta, yayin da yara miliyan 150 ke barin makaranta tun tun ba su kammala karatu ba. Har in dai ana son a yi nasara wajen yaki da talauci a duniya baki daya to dole a baiwa kowa ´yancin samun ilimi mai nagarta. A kasashen Afirka alal misali ba abin mamaki ba ne a tarar da yara sama da 100 a cikin aji guda. Hakan dai babban koma baya ne ga harkar samar da wani ilimi na a zo a gani. Wannan dai wata babbar matsala ce musamman yadda ake nunawa ´yan mata wariya a harkar ba da ilimi a wasu kasashe masu tasowa, inji Klaus Hüfner na bangaren hukumar kyautata ilimi, kimiyya da al´adu ta MDD wato UNESCO a nan Jamus. Jami´in ya ce bawa mata ilimi na taka muhimmiyar rawa wajen rage matsalar yawan al´uma barkatai, haka zalika idan yarinya mace na zuwa makaranta hakan zai rage yiwa ´yan mata aure tun suna kanana, wanda haka kuma zai rage haihuwa barkatai. Haka kuma ilimi ga ´ya mace zai taimaka mata wajen tarbiyar ´ya´yanta. Yayin da yake tofa albarkacin bakin sa game da harkar ba da ilimi a kasar Kenya, Aloys Opiyo jami´i a hukumar ba da ilimin firamare a Kenya, bayani yayi game matsalolin ba da ilimi a wannan kasa. Mista Opiyo ya ce duk da cewa sabuwar gwamnatin Kenya ta fara wani shirin ba da ilimi kyauta ga kowa da kowa, amma duk da haka akwai yara sama da miliyan biyu, musamman ´ya´yan talakawa a wannan kasa da har yanzu ba su amfana da wannan shiri ba. Wani abin da ke hana ruwa gudu bisa manufa shine iyayen yara na hana ´ya´yansu zuwa makaranta, saboda aikin gida da suke taimakawa iyayensu. Hakan kuwa ya fi faruwa ne a yankunan karkara, inda ake noma. Ga wasu iyayen kuma yiwa ´ya´yansu mata aure da wuri ya fi su tura su makaranta don samun ilimi. Wani da ake kira Simon Fah na kungiyar majami´ar protestant a Kamaru yayi nuni da cewa wannan matsala ta zama ruwan dare a yankin arewacin Kamaru, inda tun yarinya tana da shekaru 10 zuwa 11 ake yi mata aure. Saboda haka ana bukatar hadin kai tsakanin kungiyoyi daban-daban don maganin wannan matsala. Domin sai ta hanyar gudanar da shirye-shirye da ayyuka da zasu taimakawa jama´a kai tsaye za´a iya shawo kan wadannan matsalolin. To sai dai Klaus Hüfner na hukumar UNESCO ya ce ba ya goyon bayan ra´ayin kafa dokar da zata haramta kwadagon yara a kasashe masu tasowa, domin a daukacin wadannan kasashen babu wani tanadi da aka yi bisa manufa. Saboda haka kamata yayi a bullo da wasu sabbin dubaru don wayar da kan iyaye game da muhimmancin tura yaransu makaranta don samun ilimi.
 • Kwanan wata 09.02.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvlz
 • Kwanan wata 09.02.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvlz