An bayar da kyautar Nobel ta kiwon lafiya | Labarai | DW | 02.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bayar da kyautar Nobel ta kiwon lafiya

An bayar da kyautar Nobel ta kiwon lafiya ga wasu likitikitoci Amirkawa guda uku da suka gudanar da wani bincike kan tsarin aikin zuciya.

An bayar da kyautar Nobel ta kiwon lafiya ga wasu likitikitoci uku da suka gudanar da wani aikin bincike kan tsarin aikin zuciya. Likitocin Jeffrey C. Hall da Michael Rosbash da Michael W. Young, sun yi nasarar tantance tsarin aikin da zuciya take yi a cikin sa'o'i 24 da kuma yadda bugawarta ke yin tasiri a rayuwar halittu a cikin yini da kuma a cikin dare.

Likitocin sun yi nasarar gano yadda bugawar da zuciya ke yi, ke daidaita bukatun barci da na abinci da kuma yanayin zafin jikin halittu. Likitocin uku sun samu tukuyci na kudi Euro dubu 937 na Euro da za su raba a tsakaninsu.

A shekara ta 2016  Yoshinori Ohsumi wani dan kasar Japan ne ya lashe kyautar Nobel din ta kiwon lafiya a sakamakon binciken da ya gudanar kan yadda kwayoyin hallittun dan Adam ke sabunta kansu lokaci zuwa lokaci.