AN BANKADA TANADIN SIRRIN DA SHUGABA BUSH YA YI NA AFKA WA IRAQI DA YAKI. | Siyasa | DW | 19.04.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

AN BANKADA TANADIN SIRRIN DA SHUGABA BUSH YA YI NA AFKA WA IRAQI DA YAKI.

Wani sabon littafin da ya fito a Amirka a cikin wannan makon, ya bankada tanadin sirrin da shugaba Bush da mataimakansa suka yi na afka wa Iraqi da yaki. Littafin, mai suna „Plan of attack“, ya nuna cewa, ba da dadewa da kai harin kunan bakin waken ran 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 ba ne George W. Bush, ya fara tsara shirye-shiryen kai wa Iraqi hari. An ci gaba da wannan tanadin kuwa har zuwa watan Janairun shekara ta 2003. A wannan lokacin ne shugaban na Amirka ya tsai da shawarar afka wa Iraqin da yaki ko ta yaya.

Shugaba George Bush da ministan tsaronsa Donald Rumsfeld, suna kare shirin afka wa Iraqi da yaki, a wani taron maneman labarai a Texas.

Shugaba George Bush da ministan tsaronsa Donald Rumsfeld, suna kare shirin afka wa Iraqi da yaki, a wani taron maneman labarai a Texas.

Bob Woodward, wani sanannen marubuci ne a Amirka, wanda kuma ya shahara, saboda bankada labaran sirri na magudi ko kuma tabargaza, da manyan jami’an gwamnati ke da hannu ko kuma ke samun kansu a ciki. Shi ne dai wanda ya fara ba da labarin tabargazar nan ta Watergate a lokacin mulkin shugaba Nixon, abin da ya janyo saukar shugaban daga mukaminsa, bayan majalisar dattijan kasar ta yi barazanar tsige shi.

A cikin sabon littafinsa da ya buga, mai suna "Plan of attack" a turance, ko kuma shirin kai hari, Woodward ya bayyana cewa, tun cikin watan Nuwamban shekara ta 2001 ne, wato sama da watanni biyu ke nan bayana harin kunan bakin waken ran 11 ga watan Satumban wannan shekarar, shugaba Bush ya fara tanadin kai hari kan Iraqi. A ran 21 ga watan Nuwamban ne, inji Woodward, shugaban ya tuntubi ministan tsaronsa Donald Rumsfeld, don ya ba shi labarin yadda matsayin shirin kai wa Iraqi hari yake. Shirin da ma’aikatar tsaro ta Pentagon ke da shi a wannan lokacin dai, ya tsufa. Sabili da haka ne, shugaba Bush ya ba shi umarnin tsara wani sabon shirin kuma, amma bisa sharadin cewa, abin da suka tattauna sirri ne, kada ya bari kowa ya sani.

Ko shugaban kungiyar leken asirin CIA George Tenet da mai bai wa shugaba Bush shawara kan harkokin tsaro, Condoleeza Rice ma, ba su da wata masaniya game da kulleleniyar a wannan lokacin.

Marubucin ya bayyana cewa, shi da kansa ya yi fira da mutane 75, maza da mata, wadanda suke da hannu wajen tsara shirye-shiryen yakin, a cikinsu kuwa har da shugaba Bush da kansa, da kuma ministan tsaronsa Donald Rumsfeld. Amma a wani taron maneman labarai, da aka yi wa shugaba Bush tambaya game da wannan shirin, sai ya ce:-

"Ba zan iya tunawa sosai da wannan lokacin ba. Sai dai ku sake tuna mini. Amma a cikin watan Satumba, na ce mu fara mai da hankalinmu ne kan Afghanistan. Kamata ya yi muga cewa, mun kammala wannan aikin."

Shugaba Bush dai ya kara bayyana cewa, ya yi wa shirin rufa-rufa ne, don ba ya son a zarge shi da zama madugun yaki, ko kuma a janye hankalinsa daga manufar yakan ta’addanci. Amma abin da ya ba shi karfin gwiwa wajen ci gaba da tsara shirin yakan Iraqin, shi ne bayanan da kungiyar leken asirin CIA ta ba shi, da kuma hasashen da da shugaban kungiyar, George Tenet ya yi, na cewa babu shakka, shugaba Saddam Hussein, ya mallaki makaman kare-dangi. Tun cikin watan Disamban shekara ta 2001 ne, aka bai wa Janar Tommy Franks, umarnin tsara shirye-shiryen yakin. A cikin watan Fabrairun shekara ta 2002 ne kuma Bush ya ba da umarnin hambarad da Saddam Hussein. Ba da dadewa ba ne kuma, wato a cikin watan Yuli, aka girke `yan leken asirin kungiyar CIAn a Iraqi.

Bob Woodward, ya kuma bankada cewa, mataimakin shugaban kasar Amirkan Dick Cheney da mukaddashin ministan tsaron kasar Paul Wolfowitz, na cikin wadanda suka ba da kaimi wajen ganin cewa, an ci gaba da shirin yakan Iraqin.

A wannan lokacin dai, inji Woodward, sakataren harkokin wajen Amirkan, Colin Powell ne kadai, wani babban jami’in gwamnati da ya nuna adawarsa ga afka wa Iraqin da yaki. Hakan kuwa, ya janyo hauhawar tsamari tsakaninsa da mataimakin shugaban kasar Dick Cheney, har ya kai ga ma ba sa ga maciji da juna. Powell dai bai tsaya nan ba. Sai da ya gargadi shugabansa George Bush da cewar: "Idan ka kuskura ka tura dakaru zuwa kasar, wato Iraqi, to fa sai ka yi mata mulki." Abin da yake nufi a nan inji Woodward, shi ne, shiga wannan yakin kamar shiga shagon kayan tangaran ne. Duk wanda ya farfasa su, shi zai biya kudinsu. Abin da ke wakana dai kuma ke nan a halin yanzu a Iraqin.

Babbar matsalar da masu tsara shirin yakin suka fi damuwa da ita dai, ita ce yadda za su kare Firamiyan Birtaniya Tony Blair, daga kalubalen da zai huskanci, a siyasar cikin gida. Tun cikin watan Janairun shekarar ta 2003 ne, George Bush ya ba da umarnin afka wa Iraqin da yaki. Amma saboda matsin lambar da Blair ke huskanta a gida Ingila ne, aka sake komawa ga taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Woodward ya kara da cewa, a wani lokacin ma, da Amirkawan suka ga yadda nuna adawa ga yakin ke ta habaka a Birtaniya, sai shugaba Bush ya shawarci Tony Blair, da ka da ya tura dakarunsa zuwa Iraqin. Amma Blair din bai yarda da hakan ba.

 • Kwanan wata 19.04.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvkW
 • Kwanan wata 19.04.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvkW