An baiyana sakamakon zaben′yan majalisu a Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 21.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An baiyana sakamakon zaben'yan majalisu a Cote d'Ivoire

Hadin gwiwar jam'iyyun siyasar da ke yin mulki sun sami rinjaye a zaben 'yan majalisun dokokin da aka gudanar.

Kawancen jam'iyyun masu goyon bayan shugaba Alassane Ouattara sun sami kujeru 167 a cikin 254.Wannan shi ne zabe na farko da aka gudanar a kasar a karkashin sabon kudin tsarin mulki na kasar wanda shugaba Outtara ya kaddamar da kwaskwarima a kansa.'Yan adawar wadanda suka kauracewa zaben a shekara ta 2011 a yanzu zasu sake dawowa a  majalisar dokokin ta Cote d'Ivoire.