1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ku kawo karshen Boko Haram cikin watanni uku- Buhari

Mohammad Nasiru AwalAugust 13, 2015

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya umurci manyan hafsoshin dakarun kasar su kawo karshen hare-haren kungiyar Boko Haram a cikin watanni uku.

https://p.dw.com/p/1GFH5
Nigeria Symbolbild Armee Soldaten Offiziere
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Gbemiga

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sababbin hafsoshin sojan kasa, sannan ya umurce su da su kawo karshen hare-haren Boko Haram cikin watanni uku. Kungiyar wadda ta yi mubaya'a da kungiyar IS ta shafe shekaru shida tana aikata ta'asa musamman a yankin Arewa masu Gabashin Najeriya, ta'asar da ta kai ga salwantar rayuka fiye da 15,000.

Buhari ya fada wa hafsoshin sojin a Abuja cewa dole su zage dantse, su hada karfi da sauran masu ruwa da tsaki don samar da wani gagarumin aiki da zai kai ga samun sakamakon da ake bukata na kawo karshen tarzomar cikin watanni uku.

Buhari wanda ya hau kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu ya gaggauta maye gurbin shugabannin rundunar sojan kasa da na sama da na ruwa da kuma shugaban dakarun tsaro a wani matakin sake dubarun yaki da Boko Haram.