An ba da umarnin sakin wani ɗan adawa a Sudan | Labarai | DW | 02.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ba da umarnin sakin wani ɗan adawa a Sudan

Gwamnatin Sudan ta ba da umarnin sakin wani shugaban wata ƙaramar jam´iyar ´yan adawa ta ƙasar. Kamfanin dillancin labarun hukuma SUNA ya rawaito cewa an janye dukkan caje-cajen da aka yiwa Mubarak al-Fadil shugaban jam´iyar neman sauyi ta Umma Party for Renewal and Reform. A cikin watan yuli aka kama shi tare da wasu mutane 30 galibi tsofaffin sojoji sannan a watan da ya gabata aka tuhume su da yunkurin kifar da gwamnati. A yau aka shirya fara yi musu shari´a amma aka ɗage zaman kotun. Kawo yanzu ba a san dalilin sakin na su ba.