An ba da sakamakon zaben ′yan majalisa a Bangui | Labarai | DW | 22.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ba da sakamakon zaben 'yan majalisa a Bangui

Rahotanni daga Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya na cewa an samu zaben 'yan majalisa 43 tun zagayen farko daga cikin 'yan majalisu 140 da za su wakilci 'yan kasar a majalisa.

A ranar 14 ga wannan watan ne dai na Febrairu aka gudanar da zagayan farko na zaben 'yan majalisun kasar, wanda aka hada shi da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da dan takara Faustin Archange Touadéra ya lashe. Daga cikin wadanda suka samu lashe kujerun 'yan takaran na majalisa har da Martin Ziguélé da ke a matsayin shugaban jam'iyyar MLPC da Jean-Michel Mandaba na jam'iyyar PGD inda ya samu kujerar ta dan majalisa daga yankin Bamingui ta Arewa.

Akwai kuma wasu manyan 'yan siyasar kasar kamar su Bertin Béa na jam'iyyar Kwa Na Kwa, da Emilie Epaye tsofuwar minista da suma suka ci zaben. Sauran kujerun 'yan majalisun dai za a sanar da su ne bayan zagaye na biyu na zaben wanda ba a sanar da ranar yin sa ba kayo yanzu.