An ba da sakamakon kuri´ar raba gardama na larduna 13 daga cikin 18 a Iraki | Labarai | DW | 22.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ba da sakamakon kuri´ar raba gardama na larduna 13 daga cikin 18 a Iraki

Mako daya bayan kuri´ar raba gardama da aka gudanar akan sabon kundin tsarin mulkin Iraqi, hukumar zaben kasar ta ba da sakamakon farko na larduna 13 daga cikin 18 na kasar baki daya. Sakamakon ya nunar da cewa an amince da kundin tsarin mulkin a larduna 12 yayin da mabiya sunni a lardin Salaheddin ne kadai suka nuna rashin amincewarsu da sabon tsarin mulkin. Wata sanarwa da hukumar zaben ta bayar ta ce ana sake gudanar da bincike akan zargin da aka yi na aringizo kuri´u a wasu larduna biyar, kuma nan da kwanaki kalilan masu zuwa za´a bayana sakamakon su. Ana iya yin watsi da kundin tsarin mulkin idan akalla kashi 2 cikin 3 na masu zabe a larduna 3 fiye da 3 suka nuna adawa.