1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ba da kyautar Nobel ga ICAN

Abdourahamane Hassane
October 6, 2017

An ba da kyautar Nobel ta yaki da makaman nulkiya ta shekara ta 2017 ga wasu hadin gwiwar kungiyoyin masu fafutukar ganin an kawo karshen makaman nulkiya a duniya watau ICAN.

https://p.dw.com/p/2lNKT
Friedensnobelpreis 2017 ICAN  Beatrice Fihn Direktorin
Hoto: Reuters/D. Balibouse

An dai bai wa hadin gwiwar kungiyoyin masu fafutukar kyautar, saboda gwagwarmayar da suke yi na ganin an lallata makaman kare dangin na Iran da Koriya ta Arewa wadanda suka janyo ce-ce ku-ce a duniya. Hadin gwiwar kungiyoyin dai  na duniya na ICAN sun taka rawa wajen matsa kaimi aka haramta yin amfanin da makamin kare dangi na Atom wanda kasashe 122 suka rataba hannu a kan yarjejeniyar a cikin watan Yuli da ya gabata.