An amince da sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a Iraki | Labarai | DW | 20.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An amince da sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a Iraki

An rantsad da sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a Iraqi a wani zama na musamman da majalisar dokoki ta yi yau asabar. An rantsad da gwamnatin ne bayan da majalisar ta amince da majalisar ministocin FM Nuri al-Maliki da kuma shirye shiryen gwamnatinsa. Amincewa da gwamnatin na matsayin wani buri da Amirka ke fatan cimma na rage tashe tashen hankula a fadin kasar ta Iraqi. A cikin jawabinsa na farko da yayiwa majalisar al-Maliki ya ce babban batun da gwamnatinsa zata fi mayar da hankali akai shi ne maido da zaman lafiya da tsaro.

To sai dai har yanzu ba´a nada ministocin cikin gida da na tsaro ba. Ko da yake Maliki da da kuma mataimakinsa Salam al-Zubai zasu rike wadannan mukaman na wucin gadi. Wannan ci-gaban a fagen siyasa ya zo ne sa´o´i kalilan bayan wani harin bam da aka kai a birnin Bagadaza, wanda ya halaka akalla mutane 19 sannan wasu 58 suka jikata. Bam din ya fashe ne a tsakanin wani gungun ´yan shi´a dake neman aiki.