1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An albarkaci sakamakon karshe na zaben ´yan majalisar dattijan Italiya

April 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv16

Wata kotun daukaka kara a Italiya ta albarkaci sakamakon karshe na zaben ´yan majalisar dattijan kasar Italiya, abin da ya tabbatar da rinjayen kujeru biyu ga jam´iyar masu matsakaicin ra´ayi karkashin jagoranci Romano Prodi. Tabbatar da sakamakon kuri´un da ´yan Italiya dake kasar waje suka kada shi ne mataki na karshe na tabbatar da sakamakon zaben ´yan majalisar dattijan da ya gudana a ranaku 9 da 10 na wannan wata na afrilu. Duk da wannan tabbaci kuwa FM Silvio Berlusconi ya ki amincewa da shan kaye duk da cewa ya fara maganar kafa wata gwamnati karkashin Prodi.

Yayin da yake magana a gaban magyoa bayan sa Berlusconi cewa yayi:

O-Ton 1: zan kasance a bayan fage na wani gajeren lokaci a karkashin gwamnatin Prodi, bayan haka gwamnatin kawance karkashin jagoranci na zata dawo kan mulki.”