An aiwatar da hukuncin kisa kan mutane 15 a Afghanistan | Labarai | DW | 08.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An aiwatar da hukuncin kisa kan mutane 15 a Afghanistan

Kasar Afghanistan ta zartas da hukunci kisa kan wasu firsinoni 15 karon farko cikin shekaru 3. Wannan adadin shi ne mafi yawa da aka aiwatar da wannan hukuncin a kan wasu tun bayan kifar da gwamnatin Taliban a shekara ta 2001. Mutanen dai an same su da laifuka iri daban daban ciki har da kisan baki ´yan jarida da wani ma´aikacin MDD da ´yan sanda da fashi da makami da kuma yin garkuwa da mutane. A cikin wata sanarwa tawagar MDD a Afghanistan ta ce da ya fi kyau in da gwamnati ta girmama wata yarjejeniyar da aka cimma akan dakatar da hukunci kisa.