An ɗage dokar ta bace a Irak | Labarai | DW | 07.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ɗage dokar ta bace a Irak

Hukumomin ƙasar Iraki, sun dage dokar ta bacen da su ka kafa, bayan hanke hukunci kissa, ga tsofan shugaban kasa Saddam Hussain.

Duk da wannan hukunci mai tsanani, yau ne kuma Saddam zai sake gurfana gaban kotu, tare da mukaraban sa guda 6.

A wannan karo, ana zargin su, da aikatan kissan kiyasu, ga ƙurdawa na yankin Anfal.

A shekara ta 1987 zuwa 1988 Saddam Hussain,ya umurci yin ruwa gaz, ga ƙurdawa, wanda a sakamakon, hakan mutane dubu 180, su ka rasa rayuka.

A ɓangaren hare haren kuwa, sai abin da ya ci gaba.

A na kyauttata zaton ma, su ƙara tsamari, bayan hukuncin da a ka yankewa Saddam Husain.