An ɗage ɗaurin talala da ake yiwa Benazir Bhutto | Labarai | DW | 16.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ɗage ɗaurin talala da ake yiwa Benazir Bhutto

Hukumomi a ƙasar Pakistan sun saki shugabar ´yan adawa Benazir Bhutto daga ɗaurin talala. Hakan ya zo ne sa´o´i ƙalilan bayan naɗa Firaministan riƙon ƙwarya a wani matakin farko na shirye shiryen gudanar da zaben kasa baki ɗaya. Gandurobobi sun bar gidan dake birnin Lahore na gabashin ƙasar, inda aka tsare Bhutto don hana ta jagorantar wani macin masu radin kafa demokuraɗiyya dake adawa da dokar ta ɓaci da shugaba Pervez Musharraf ya kafa. Shugaban Musharraf dai ya yi alkawarin shirya zabe a ranar 9 ga watan janeru kuma yanzu haka ya nada shugaban majalisar dattawa Mohammadmian Soomro a matsayin FM riƙon ƙwarya. A kuma halin da ake ciki Bhutto da tsohon FM Nawaz Shariff dake gudun hijira sun amince sun haɗa ƙarfi da ƙarfe don fatattakar shugaba Musharraf.