An ƙulla dangantar diplomatia tsakanin China da Tchad | Labarai | DW | 07.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ƙulla dangantar diplomatia tsakanin China da Tchad

Ƙasar Tchadi ta yanke shawara sake ƙulla hulɗoɗin diplomatia da China, abun da take, ke nufin katse dangantaka, ta da tsibirin Taiwan.

A ƙarshen makon da ya gabata, ministan harakokin wajen Tschad,, ya gana da takwaran sa na Taiwan, domin bayyana masa wannan labari, da ya baƙanta rayukan hukumominTai- Pey.

A hukumce, jiya ne Shugaban Idriss Deby, ya hiddo sanarwar sake ƙulla hulɗoɗi da China, bayan katsewar su, tun shekara ta 1997.

Wannan al´amari ya wakana, a yayin da Praministan Taiwan, Tseng Chang,ke shirin kai ziyara ranar talata, a birnin N Djamena , domin halartar rantsar da shugaban ƙasa Idriss Deby Itno, da ya yi tazarce a watan Mayu da ya gabata.

To amma a halin yanzu Praministan ya fasa a wannan ziayara.

A dalili da kustawar da Sin a Afrika, ƙasashe da dama sun bayyana raba gari, da Taiwan a wannan nahiya.

A halin yanzu, ƙasashe 5 kaɗai na Afrika, ke ci gaba da hulɗoɗi da Taiwan, wato Burkina Faso, Gambia, Malawi, Sawziland ,da Sao Tome da Principe.