1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama´a akan addinin Islama

Mohammad AwalJune 30, 2007

Shirin da ake yiwa laƙabi da One Global Family wasu matasa muslmi ne a birnin Dortmund suka ƙaddamar da shi.

https://p.dw.com/p/BvSo
Musulmi da Kirista a Jamus
Musulmi da Kirista a JamusHoto: picture-alliance/dpa

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taba Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka sahfi addinai, al´adu da zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

A halin da ake ciki da yawa daga cikin musulmi matasa a nan Jamus suna kaddamar da sabbin shirye shirye a wani mataki na gabatarwa al´uma da addinin Islama ta hanya mafi sauki kuma sassauci. Alal misali a birnin Dortmund dake yammacin nan Jamus an kaddamar da wani shiri mai taken One Global Family wato Iyalin duniya daya don tafiyar da wani shiri mai kayatarwa. Wannan shiri kuwa ya tanadi yin amfani da kida da wasannin kwaikwayo da yin wasu ayyukan hadin kai don gabatar da addinin Islama a tsakanin al´umar wannan kasa. Filin na yau zai duba irin aikace aikacen da shirin na One Global Family ya tanadar akan addinin na Islama a nan kasar. Masu sauraro MNA ke muku lale marhabin a cikin shirin.

1. O-Ton Atmo:

Gun wani taron matasa ke nan na shirin na One Global Family a wata unguwa dake arewacin birnin Dortmund. Wasu matasa ne su 4 masu shekarun haihuwa daga 20 zuwa 25 akan wani dandamali suke raira wakar kungiyar kuma suna cashewa. Har izuwa wannan lokaci kuwa matasan suna koyan rawa ne gabanin wani wasa na farko da zasu yi a bainar jama´a, inda zasu gabatar da shirin na su. Burin su shine gabatar da wani kyakkyawan hoton addinin Islama ga al´umar Jamus, wadanda daukacin su ke da mummunar fahimta da wannan addini.

Youssef Lawur mai shekaru 29 a duniya wanda iyayensa suka yi kaura daga Marokko zuwa Jamus shekaru masu yawa da suka gabata, shi ne shugaban sabon shirin na One Global Family.

2. O-Ton Yussef Laawar:

“Hanya mafi dacewa wajen dinke baraka ko samun fahimtar juna ita ce ta wasannin motsa jiki ko wake-wake. Ta haka an fi samun hadin kan jama´a. Wannan dai ita ce dabarar mu.”

Shi dai Youssef da kannensa Said wanda shi ma yake cikin shirin suka fara gabatar da wannan shawara. Kimanin shekara daya da ta gabata ´ya´uwan junan su biyu masu kokari wadanda suka fito daga wani gida in da musulunci yayi kwai ya kyankyashe, suka fara tattara shawarwari da bayyanai kan hanya mafi dacewa wajen amfani da wake-wake fayafayen bidiyo da wasan kwaikwayo don gabatar da addinin Islama a tsakanin jama´a.

Alal misali gabanin su kaddamar da bidiyon su na farko, Youssef da Sa´eed sun nemi jin ra´ayin Jamusawa game da musulunci da musulmi baki daya.

3. + 4. O-Ton Atmo:

Wannan dai wani sashe ne na wasan kwaikwayo na tsawon sa´o´i 6 da Youssef da Sa´id da sauran matasa na shirin One Global Family zasu gabatar lokacin da zasu yi wani yawon fadakarwa game da zaman cude ni in cude ka tsakanin mabiya addinai daban daban a Jamus. Ban da wasan kwaikwayo shirin ya kuma kunshi kida da wake wake na zamani don yin bayani dalla dalla game da addinin Islama.

5. O-Ton Said Laaour:

“Wannan wasan kwaikwayo ya kunshi dukkan abubuwan dake faruwa a zahiri, musamman abubuwan da mu kanmu da sauran abokane ko ´yan´uwa suke haduwa da su a rayuwarmu ta yau da kullum. Wato abubuwa ne na gaskiya ba almara ba. Suna bayani game da matsaloli da halin kakani-kayi da musulmi ko wani dan Adam ke cin karo da su saboda launin fatar jikinsa ko addininsa a rayuwarsa ta yau da kullum.”

Lawur da Said sun kuduri aniyar gabatar da shirye shirye masu kayatarwa ga jama´a. A ma halin da ake ciki wasu musulmin sun nuna sha´awar ba da gudunmawa a shirye shiryen. Wato kamar Mimoun mai shekaru 20 da haihuwa wanda duk da shakkun da ya nuna da farko amma ya yi na´am da goron gayyata da Said ya ba shi na shiga kungiyar.

6. O-Ton Mimoun:

“Da farko dai tunani na shi ne ko za´a iya hada wasan kwaikwayo, kade-kade da wake-wake a bainar jama´a da addinin Islama. To amma gaskiya ban sani ba. Ko da yake na fada masa cewa ra´ayin babu laifi amma ina son ya bani lokaci kafin in ba shi amsa. Bayan na koma gida na yi tunani mai zurfi, inda na ga cewa ai da ma ina halartan taruka daban daban game da zamantakewa da dai sauransu. Saboda haka ba da bata lokaci ba sai na yanke shawarar shiga cikin wannan shiri tun wani bai rigaye ni ba.”

A cikin ´yan makonni masu zuwa Youssef da Said da sauran matasan zasu fara bayyana a gaban jama´a musamman a gaban kungiyoyin dake tafiyar da aikin irin na kyautata zamantakewa. Said Lawur ya nunar da cewa.

7. O-Ton Saida Laaour:

“Saboda dalilai na yawan aikata laifuka, ba safai ake samun matasa a cikin irin wadannan kungiyoyi ba. Sun yi kokarin gabatar da shirye shirye makamancin na mu amma duk da haka matasan ba sa halarta kuma ba sa sauraran su. Mu dai shirin mu ya kunshi abubuwa da ke burge matasa.”

Youssef da Said na fatan cewa shirin na One Global Family zai samu karbuwa a tsakanin matasa. Da wannan shiri zasu yi kokarin gabatar da sako na wani kyakkyawan matsayi na addinin Islama. Youssef ya nunar a fili cewa ba zasu mayar da wani saniyar ware ba.

8. O-Ton Youssef:

“Burin mu shi ne hada kawunan musulmi da wadanda musulmi ba. Ba zamu tilasta ma wani shiga addinin mu ba. Zamu nuna musu cewa ba a banza suka shiga cikin wannan shiri ba, manufa shi ne a taimaki juna kuma a cimma burin da aka sa a gaba. Shirin ya na maraba da kowa da kowa saboda haka ne ma ba mu ba shi sunan wani addini ba. Zaman lafiya muke so a ko-ina cikin duniya.”