1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka zata sauya alkibla dangane da rikicin Iraki

Shugaban Amirka GWB ya ba da sanarwar daukar sabuwar alkibla a manufofin kasarsa dangane da yankin GTT. To sai dai a gun wani taron manema labarai da suka yi da FM Birtaniya Tony Blair a birnin Washington, shugaba Bush ya ki fitowa fili ya bayyana ra´ayinsa game da wasu batuttuwa da hukumar nan ta Baker ta ba ta shawara a kai. Hukumar wadda ta kunshi wakilai daga jam´iyu daban daban ta ba da shawara da a shigar da kasashen Syria da Iran a tattaunawar da ake game da halin da ake ciki a Iraqi. A wani lokaci yau Bush zai gana da shugabannin jam´iyun Republicans da Democrats a majalisun dokokin Amirka, inda zai nemi ra´ayoyinsu game da rahoton na tsofaffin ´yan siyasar Amirka.