Amurka zata mikawa Iraki ragamar tsaro | Labarai | DW | 04.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka zata mikawa Iraki ragamar tsaro

Amurka da Iraki na fatan rattaba hannu akan yarjejeniyar mikawa dakarun sojin kasar ragamar tafiyar da harkokin tsaro.Mikawa dakarun Irakin ragamar tsaro bayan horar dasu da Amurkan ta jagoranta,na bangaren shirye shiryemn washinton na janye dakarunta kimanin dubu 140,dake Irakin.An jinkirta bukin rattaba hannu a yarjejeniyar,wadda ya kamata a gudanar a jiya asabar ,adangane da wasu kalamai dake kunshe cikin takadun kan dangantakar sabbin sojojin.Kakakin gwamnatin Bagadaza Ali al-Dabbagh ya fadawa manema labaru cewa,a halin yanzu an samu daidaituwa kan batun tsakanin bangarorin biyu,inda akesaran rattaba hannu akan yarjejeniyar akarshen wannan makon.

A hannu guda kuma dakarun tsaron Irakin sun gano gawawwakin mutane 28 ,a wani makeken kabari a Tarkalan,kusa da birnin Kirkut dake arewaci.

 • Kwanan wata 04.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5Y
 • Kwanan wata 04.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5Y