Amurka zata canza matakan da take aiwatarwa a Irak | Labarai | DW | 12.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka zata canza matakan da take aiwatarwa a Irak

Rahotanni daga Amurka na nuni da cewa da alama mahukuntan kasar, zasu canza ire iren matakan da suke aiwatarwa a Iraqi.

A cikin jawabin sa na mako mako, shugaba Bush ya tabbatar da cewa sabon ministan harkokin tsaron kasar, wato Robert Gates, mutum ne mai hangen nesa, da zai iya kawo sabbin matakai da zasu kai ga cimma nasarar da aka sa a gaba.

Bugu da kari shugaba Bush, ya kuma yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da yan jam´iyyar democrat, wajen yaki da ayyukan ta´addanci.

Daukar wannan mataki dai ya biyo bayan, nasarar da jam´iyyar ne ta samu na jagorantar majalisun dokokin kasar biyu, a zabubbuka da aka gudanar a ranar talatar data gabata.