1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka za ta aike da wasu dakaru na musamman Iraki

Amurka na shirye-shiryen aikewa da wasu sojojin ta na musamnan zuwa kasar Iraki domin yakar kungiyar Is ta hanyar jagorantar kai hare-hare akan iyakar kasar da Syriya.

Sakataren harkokin tsaron Amurkan Ashton Carter a yayin da yake magana a gaban kwamitin ayyukan soji yayi nuni da cewar.

Ta kara dorawa kan yakar kungiyar zamu aike da wasu dakaru a bisa umarnin shugaba Obama don murkushe ayyukan Is a Iraki,wadan nan dakurin na musamman nada ikon kwace yankunan da kungiyar ta kwace.

kalaman sakataren tsaron Amirkan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da 'yan majalisar Britaniya suke shirye-shiryen tafka muhawara ne akan ko shin sojojin kasar zasu taka rawa kan yakar Is a Syriya ne ko a'a.