Amurka tayi watsi da tayin maslaha na bin Laden | Labarai | DW | 20.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka tayi watsi da tayin maslaha na bin Laden

Kasar Amurka tayi watsi da tayin sasanta tsakani da Osama bin Laden aka ce ya mika mata cikin wani sabon sako da ya aikewa alummar amurka da aka nuna a gidan TV na Aljazeera,

inda a ciki aka ji yana gargadin kaiwa sabbin hare hare akan kasar Amurka,amma ya mika hannun sasantawa ga jamaar Amurkan muddin Amurkan ta janye daga Iraqi da Afghanistan.

Kakakin fadar gwamnatin Amurka ta white house,Scott Mclellan yace kasar Amurka ba zata tattauna da yan taadda ba.

Wannan dai shine karo na farko da aka ji daga Osama tun 2004.