Amurka tayi watsi da kiran Biritaniya na rufe Guantanamo Bay | Labarai | DW | 11.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka tayi watsi da kiran Biritaniya na rufe Guantanamo Bay

Amurka tayi watsi da kiran da wani babban lauya mai bawa gwamnatin Biritaniya shawara a fannin shari´a, yayi na ta rufe gidan yarin Guantanamo Bay dake kasar Cuba.

Kafafen yada labaru sun rawairo jami´an kasar ta Amurka na cewa gidan yarin na Guntanamo Bay na dauke da fursunoni wadanda suka aikata miyagun laifuffuka, wanda sako su ka iya haifar da zaune tsaye ga duniya.

Wannan dai kalami na jami´an na Amurka yazo ne bayan da babban atoni na Biritaniya wato Lord Goldsmith ya bukaci Amurka data rufe gidan yarin , bisa dalilin cewa gidan yarin alama ce ta rashin adalci.

A can baya dai idan za´a iya tunawa Faraminista Tony Blair ya bukaci mahukuntan na Amurka dasu rufe gvidan yarin na Guantanamo Bay, bisa zarge zargen take hakkin bil adama da akeyi ga fursunoni.

Ya zuwa yanzu dai an ce akwai fursunoni kusan 490 da ake tsare dasu a gidan yarin na Guantanamo Bay bisa zargin gudanar da aiyukakkan ta´addanci. Rahotanni dai sun nunar da cewa da yawa yawan fursunonin ana tsare dasu ne ba tare da an tuhume su zargin da ake musu ba.