Amurka tace bai kamata a bata lokaci wajen yanke shawara kan Iran ba | Labarai | DW | 24.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka tace bai kamata a bata lokaci wajen yanke shawara kan Iran ba

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta baiyana cewa,bai kamata membobin komitin sulhu su bata lokaci ba wajen yanke shawara akan shirin nukiliya na kasar Iran.

Kasashen Rasha da Sin dai sunki amincewa su sanya hannu akan wata sanarawa dake dauke da kalamai masu zafi akan shirin nukiliya na Iran,wanda kasashen Amurka Burtaniya da Faransa suka shawarta,wadda ta bukaci Iran ta dakatar da inganta sinadaren uraniyum.

Tattaunawar tsakanin membobin din din din 5 na komitin sulhun ya samu cikas,game da wanna sanarwa wadda magoya bayan kasar Iran suke gani wani share fage ne na lakaba mata takunkumi,wanda kuma su basa goyon baya.

Kowane memba dai yana da ikon hawa kujerar naki game da duk wata shawara da aka yanke.

Yanzu haka Rice ta shirya tattaunawa yau jumaa da takwararnta na Rasha don kawo karshen wannan kiki kaka.