Amurka tace ba azta sa ido ta bar Iran da shirinta ba | Labarai | DW | 22.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka tace ba azta sa ido ta bar Iran da shirinta ba

Mataimakin shugaban kasar Amurka Dick Chaney ya yi gargadin cewa gwamnatin Amurka ba zata zuba ido ta ga Iran ta ci gaba da shirinta na nukiliya ba.Da yake magana wajen wani babban taro kann manufar yankin gabas ta tsakiya,Cheney yace gwamnatin Iran ita ke kawo cikas ga zaman lafiya.ya kuma nanata zargi da Amurkan take yiwa Iran cewa tana marawa yan sojojin sa kai a Iraki baya.Chenye yayi wadanan kalaman ne kwanaki kadan bayan shugaban Amurka George Bush yayi kashedin barkewar yakin duniya na uku muddin dai an bar Iran ta mallaki makaman nukiliya.A nata bangare gwamnatin Iran tace shirinta na nukiliya ba shi da alaka da makamai.