Amurka ta yi kira ga Koriya ta Arewa ta martaba yarjejeniya | Labarai | DW | 15.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta yi kira ga Koriya ta Arewa ta martaba yarjejeniya

Amurka ta ce wajibi ne Koriya ta arewa ta martaba yarjejeniyar da ta sanyawa hannu na rufe tashar nukiliyar ta, ta kuma kyale jamaián binciken na majalisar dinkin duniya zuwa kasar. Wannan bukatar dai ta zo ne bayan karewar waádin da aka debawa Pyongyang na rufe tashar nukiliyar ya kare a jiya ba tare da alamun zata aiwatar da umarnin rufe tashar ba. A taron kasashe shidda da ya gudana a cikin watan Fabrairu a birnin Beijin, Koriya ta arewa ta sanya hannu a kan yarjejeniyar rufe tashar nukiliyar, to amma daga bisani ta ce ba zata aiwatar da komai ba har sai kudaden ta dala miliyan 25 da Amurka ta rike sun shiga hannu ta tukunna. Amurkan dai ta ce tuni ta sakin kudin a saboda haka akwai bukatar Pyongyang ta hanzarta cika sharudan da aka cimma a yarjejeniyar. A hannu guda dai babban mashawarcin Koriya ta arewan yace gwamnatin na bukatar karin kwanaki talatin domin rufe tashar nukiliyar.