Amurka ta yi kira da a binciki zargin magudi a zaben Rasha | Labarai | DW | 03.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta yi kira da a binciki zargin magudi a zaben Rasha

Gwamnatin Amurka ta yi kira ga hukumomin Rasha da su yi bincike kan zargin maguɗi a zaɓen da aka gudanar.Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka ta White House Dana Perino tace rahotanni daga Rasha sun baiyana cewa an tafka maguɗi a zaɓen.Kodayake tace ba zasu yanke hukunci kan zaɓen ba. Jamiyar Putin ta United Russia Party ta lashe zaɓen majalisar wakilai da kashi biyu bisa uku na kuri`u da aka kaɗa wanda ya baiwa magoya bayan Putin damar aiwatar da canje canje cikin kundin tsarin mulkin ƙasar.