1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta yi kashedi ga shugabannin Iraqi su sasanta junan su

October 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuhC

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta gargaɗi shugabannin ƙasar Iraqi da cewa suna da taƙaitaccen lokaci ne fa na sasanta tsakanin su, tana mai cewa ko kaɗan ba zaá lamunta da cigaban tarzoma da ƙaruwar tashin hankula ba. A ziyarar ba zata da ta kai ƙasar Iraqin, Condoleezza Rice ta nanata cewa gwamnatin Bush bata haínci Amurkawa ba a game da matsayin ta a Iraqi da kuma kuɗaɗen da take kashewa wajen yaƙin, tana mai cewa hakika wannan jan aiki ne mawuyaci. Shekaru uku bayan da Amurka ta hamɓarar da gwamnatin Saddam Hussaini, ƙasar Iraqi ta tsunduma cikin rikicin da yaƙi ci yaƙi cinyewa a tsakanin mabiya ɗarikun sunni dana shiá, abun da P/M ƙasar Nuri al-Maliki yake ta kokarin shawo kan sa ta hanyar kafa gwamnatin hadin kan ƙasa. Bayan ganawa da shugaban ƙasar Iraqi Jalala Talabani da P/M Nuri al-Maliki, Condoleezza Rice ta kuma gana da shugabannin jamíyu na ɓangaren sunni dana shiá da kuma na ƙurdawa