1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta yi amai ta lashe

Hauwa Abubakar AjejeAugust 10, 2005

Kasar Amurka ta janye kudirinta na maida hambararren shugaban Mauritania bisa mulki.

https://p.dw.com/p/BvaX
Bush
BushHoto: AP

Kasar Amurka ta janye kudirinta na mayarda Hambararren shugaban kasar Mauritania bisa karagar mulkinsa,tana mai fadin cewa zata matsawa gwamnatin sojin da ta kwaci mulkin da ta gaggauta mika mulki ga farar hula.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Adam Ereli,ya baiyanawa manema labarai a birnin Washington cewa, sojojin da suke mulkin yanzu da su ya kamata a tattauna, saboda sune suke zartar da kudurori a kasar yanzu,kuma kasar Amurka tana kokarin ganin cewa sun dauki matakai da suka dace.

A matsayin wani bangare na yaki da ta’adanci na,shugaba Bush,Amurkan tana aikewa da jamianta domin horas da jamian sojin Mauritania da ma na wasu kasashe da ke yankin sahara domin shirin ko ta kwana ko kuma dakile yan gwagwarmaya da ke kasashen sahara.

Kasar Amurkan da Kungiyar Taraiyar Turai da Kungiyar Taraiyar Afrika da farko sun yi Allah wadai da wannan juyin mulki,wadda da farko Amurkan ta nemi a maida Muawiya bisa mulkinsa.

To amma yan adawa da kuma yan jamiyar shi Muawiya kansa suna goyon bayan wannan juyin mulkin,hakazalika jama’ar kasar sun kwarara kan tituna suna masu baiyana farin cikinsu game da juyin mulkin.

Haka itama kungiyar taraiyar Afrika AU a karshen ganawarta da shugabannin sojin yau tace ta bukacesu da su gaggauta shirya zabe, hakazalika tana nan kan bakarta ta dakatar da Mauritania daga cikin kungiyar ta AU.

A yammacin jiya Prime ministan farar hula da aka nada Sidi Mohammad ould Boubakar, ya kira taron manyan jamian gwamnatin kasar tare da nufin kafa sabuwar gawmanati cikin wannan mako.

Yan kasar Mauritania da dama dai sun soki lamirin kasashen duniya da suke nuna damuwarsu game da wannan juyin mulkin,domin a cewarsu kasashen sun kame bakinsu a lokacinda Taya yake musu mulkin danniya.

Muawiya ould Taya dai ya mayarda kasar ta Mauritania saniyar ware cikin kasashen Afrika da ke kusa da sahara,saboda korar dubban bakar fata yan Afrika da yayi daga kasar,ya kuma ware kasar daga kasashen larabawa ta hanyar kafa huldar diplomasiya da kasar Israila.

Majalisar mulkin sojin mai membobi 17 wadda ta kwaci mulkin daga hannun Muawiya Sid Ahmed Ould taya da yayiwa kasar mulkin danniya na tsawon shekaru 21,ta kara samun goyon bayan yan kasar ne yayinda ta saki wasu fursunonin siyasa tare da kiran taro da dukkan bangarori na kasar ta kuma alkawarta mika mulki ga hannun fara hula nan da shekaru biyu masu zuwa.