Amurka ta tsaurara tsaro a kan iyakar ta da Mexico | Labarai | DW | 16.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta tsaurara tsaro a kan iyakar ta da Mexico

Shugaban Amurka George W Bush ya sanar da aniyar tura dakarun soji 6,000 zuwa kan iyakar Amurka da Mexico. Yace akwai bukatar gaggawa ta kare kwararowar bakin haure daga kan iyakar zuwa cikin Amuka. Bush ya baiyana kudirin ne a wani jawabi da ya yi wanda aka nuna ta akwatunan Talabijin. Sai dai kuma a waje guda jawabin ya haifar da kakkausar suka daga yan ci rani wadanda ke baiyana cewa hakan ba zai razana su ba. Ita kuwa kasar Mexico ta baiyana fatan cewa matakin zai kai ga yin gagarumin garanbawul a dokokin shige da fice.