Amurka ta sha kaye a kwamitin tsaro na MDD | Siyasa | DW | 24.06.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amurka ta sha kaye a kwamitin tsaro na MDD

Yayan kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya sun fara juyawa Amurka baya a dangane da kariyar data nema na sojijinta dake aiki a kasashen ketare

default

.:Kasar ta Amurkan dai ta dauki wannan matakin ne a jiya a yayin da take kallobn cewa batun ba zai sami karbuwa ba daga yayan kwamitin na MDD :kamar dai yarda kanfanin dillancin labarai na IPS ya ruwaito cewa a kalla cikin kasashe 15 na kwamitin sama da 11 sun nuna adawa da shirin na Amurka ..Daya daga cikin jamian kotun kasa da kasa Bill Pace ya tabbatarwa da Ips cewa a yanzu haka Amurka zata fuskanci kauracewa wannan batu daga yayan kwamitin idan har ta kuskura ta mika shi domin amincewa ..Cikin kasashen da suka fito kirikiri domin nuna wannan adawa har da Kasar China da faransa wadanda keda kujerar din din din a kwamitin tsaro na wannan majalisa .Jakadan kasar ta China kuwa a wannan majalisar ya tabbatar da haka a wata hira daya yi da manema labaru a kann haka .. wAta Majiya na cewa kasashen dake marawa Amurka baya sune kasashen Rasha da Britaniya .To sai dai a daura da haka jakadan kasar Amurka a MDD James Cunnigham yace kasarsa ta janye wannan batun ne baki dayansa domin magance doguwar mahawara a tsakanin yayan kwamitin na MDd a halin da ake ciki a yanzu haka ..Shi kuwa sakatare janar na kungiyar kasa da kasa ta Am,nesty International Irene Khan yace babu wata kasa da zata haifar da tsaiko kann halarcin wannan kotu kuma a zuba mata ido .Yace wannan dai wata nasace da Zaman lafiya da karuwar arzikin kasashen duniya ta samu ne bisa wabnnan sarkakkiyar da Amurka taso ta gabatar domin son zuciyarta .Sakatare janar na Mdd Kofi Annan tun a makon daya gabata ya nuna adawa da yarda Amurka ke faman son a tsame sojojinta daga gurfana a gaban wannan kotun kamar kowane jamiiin daya keta dokar kasa da kasa .Yace bisa laakari da abun daya faru a can kasar iraq a gidan Mazan Abu Garib inda jamian tsaron Amurka suka dunga cin karensu batare da babbaka ba .Sakatare janar yace idan har hankali ya bace hankali ne ke nemansa yace halin rayuwa a iraq ya nunar a fili yarda yayan kwamitin zasu nuna adawa da wannan matakin da Amurka ke neman dauka domin neman kariya ga dakarunta dake kasashen ketare musamman a fagen daga ko kuma kwantar da tarzoma a sassa daban daban na wannan duniya ..Kamar dai yarda kamnfanin dillancin labarai na Ips yace dakarun amurka a yankuna da dama sun aiwatar da cin zarafin bil adama wanda hakan ka iya gurfanar dasu a gaban wannan kotun kasa da kasa .Bayan 30 ga wannan watan kuwa dakarun kawance a can kasar iraq zasu bi laimar wata runduna ne kamar yarda kwamitin tsaron MDD ya amince a watan daya gabata domin tabbataer da tsaro a cikin kasar ta Iraq ..Wani babban malami Farfesa John Quigley dake koyarwa a can jihar Ohio a Amuirka yace bisa cin kashin da dakarun Amurka sukayi a kasar iraq ya zama wajibi a gurfamnar dasu kamar yarda Doka ta tsara .

 • Kwanan wata 24.06.2004
 • Mawallafi Mansou Bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvij
 • Kwanan wata 24.06.2004
 • Mawallafi Mansou Bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvij