1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta sanarda tsare masu shirin kai mata hari

An tsare wasu mutane 7 game da zargin shirin kai hari akan gini mafi tsawo a kasar Amurka,Chicago Towers.

Jamian hukumar FBI suka suka tsare wadannan mutane bayan farmaki da suka kai a arewacin Miami.

Cikin wadanda aka tsaren kuwa,5 daga cikinsu yan kasar Amurka ne,daya kuma bako ne dake da takardar zama sai kuma na biyun dan kasar Haiti,wanda bashi da takardun shiga kasar ta Amurka.

Kafofin yada labarai na Amurkan sun bada rahoton cewa,wadannan mutane suna tattauna batun kai harin bam ne kana manyan gurare na Amurka a Miami da Chicago.