Amurka ta sake jan kunnen Iran game da Iraqi | Labarai | DW | 01.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta sake jan kunnen Iran game da Iraqi

Amurka tace har Iran tana taimakawa sojin sa kai yan shia a Iraqi da fasahar makamai da suke anfani da su suna kashe sojojin Amurka,tana mai kara gargadin Iran din game da sa kanta a rikicin kasar Iraqi.

Karamin sakataren harkokin wajen Amurkan Nicholas Burns yace sun tsare wasu jamian Iran da suna da hannu cikin wannan zargi.

Gwamnatin Amurkan dai tana zargin Iran da laifin kawo cikas ga kokarin kawo zaman lafiya a kasar Iraq.

Tun farko shugaban Amurka Bush ya sha alwashin cewa Amurka zata maida martani mai karfin gaske muddin Iran ta ci gaba da haddasa rikici a kasar Iraqi.

Kalaman na Bush sun kara yada hasashen yiwuwar Amurka ta kaiwa Iran hari.