Amurka ta kira taron gaggawa na komitin sulhu akan Sudan | Labarai | DW | 05.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta kira taron gaggawa na komitin sulhu akan Sudan

Kasar Amurka tayi kiran taron gaggawa na komitin sulhu,bayan takarda da gwamnatin Sudan ta aika tana mai gargadin kasashe da suke da niyyar aikewa da sojojinsu zuwa yankin Darfur cewa,yin hakan wani share fage ne na mamaye kasar.

Sudan ta aike da wasikar ga kasashe 50,wadanda suka halarci taron kasashe dake da aniyar bada gudumowar dakarunsu karkashin majalisar dinkin duniya zuwa Darfur nan gaba.

Tunda farko a yau din shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir yace zai yi maraba da duk wani taimakon kudi da kayan aiki ga dakaraun kungiyar taraiyar Afrika AU a Darfur,amma ba kasancewar sojin kasa da kasa ba,kamar yadda kasashen yammacin duniya musamman Amurka suke bukata.