Amurka ta katse mu´amulla da kungiyyar Hamas | Labarai | DW | 01.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta katse mu´amulla da kungiyyar Hamas

Amurka ta dakatar da duk wata hulda ta kut da kut da gwamnatin Palasdinawa da kungiyyar Hamas ta masu kishin Addinin Islama kewa Jagoranci.

To amma duk da haka, mahukuntan kasar sun shaidar da ci gaba da mu´amulla da wakilin gwamnatin yankin dake birnin Washinton, bisa dalilin cewa bashi da mu´amulla ta aikewa da rahoto ga ma´aikatar harkokin wajen yankin na Palasdinawa.

Bugu da kari, mahukuntan na Amurka sun kuma tabbatar da cewa zasu ci gaba da yin mu´amulla da shugaban yankin wato Mahmud Abbas.

Rahotanni dai sun nunar da cewa Mahukuntan na Amurka sun dauki wannan matakin ne a bisa dalilin kallon da suke wa kungiyyar ta Hamas a matsayin kungiyya ce ta yan ta´adda.