Amurka ta karyata azabtar da jami′in Iran | Labarai | DW | 08.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta karyata azabtar da jami'in Iran

Kasar Amurka ta karyata ikrarin da wani jami’in diplomasiya na Iran da aka Amurka ta tsare yayi cewa jamian hukumar CIA sun azabtar da shi a laokacinda suke tsare da shi a akasar ta Iraqi.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin nAmurka yace wannan farfaganda ce Iran takeyi.

Kanfanin dillancin labaru na Iran ya ruwaito jamiin na Iran Jalal Shafari yana mai fadin cewa jami’an kasar Iraqi suka sace shi tare da taimakon CIA inda suka sanya shi cikin nauioin azaba iri dabam dabam.

Shafari shine sakatare na biyu a ofishin jakadancin Iran dake birnin Bagadaza lokacinda aka tsare shi tare da abokan aikinsa 4 ana zarginsu da taimakawa sojojin sa kai a Iraqi.

An kuma sako shi ne cikin rikici na tsare sojojin Burtaniyana nan 15 a Iran.