Amurka ta kai hari kudancin Somalia | Siyasa | DW | 09.01.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amurka ta kai hari kudancin Somalia

majiyoyi daga gwamnatin Somalia sun sanarda cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a harin da Amurka ta kadadamar a Kauyen Hayo a kudancin Somalia,tana mai farautar a cewarta wasu yan kungiyar alqeda biyu da suka kai hari kan ofisoshinta na jakadanci a gabashin Afrika.

default

A karo na farko ya baiyana daya baiyana shigar Amurka cikin rikicin Somalia,jirgin saman yakin Amurka sanfurin AC 130 yayi luguden wuta akan kauyen Hayo dake kudancin Somalia a daren jiya.

Kauyen na Hayo yana a tsakanin garuruwan Afmadow da Doble ne,yankin da dakarun Habasha da Somalia sula kora mayakan islama bayan watanni shida da sukayi suna rike da Mogadishu da yawancin kudancin Somalia.

Jirgin na AC 130 wanda rundunar sojin Amurka tayi anfani da shi a Vietnam da Afghanistan da kuma Iraqi,yana dauke da naurori da a cewar jamian Amurka da zasu iya gano ainihin inda ake son kai harin.

Jamian liken asiri na kasashen Habasha da Kenya da kuma Amurkan ne dai suka baiyana cewa,mayakan islaman sun bada mafaka ga wasu yan kungiyar Alqaeda da suka kai hari kan ofisoshin jakadancin Amurka a Kenya da Tanzania a 1998.

Gwamnatin Amurkan ta sanarda sunayen mutanen uku, Fazul Abdullah Muhammad dan tsibrin Komoros da Saleh Ali Saleh Nabhan na kasar Kenya da Abu Taha al-Sudani dan kasar Sudan.

Sai dai kuma magoya bayan kotunan islaman sun karyata cewa da wadannan mutane a cikinsu,suna masu cewa Amurka ce ta kirkiro da wannan batu domin bada hujjar kai hari kasar Somalia.

Su dai mayakan islama wadanda magoya baya ne na kotunan musulunci da suke rike da Mogadishu wadanda kuma suka kawo doka da oda a birnin sun lashi takobin kai hari kan hedkwatar gwamnati dake birnin Baidoa makonni biyu da suka shige,sai dai kuma shigar sojin Habasah sukayi cikin wannan rikici ya tilasata masu barin yankin na Baidoa inda suka nufi Kismayu kusa da bakin iyaka kasar Kenya.

Yanzu haka dai daruruwan mayakan islaman suna boye ne cikin duwatsu da dazuzzukan kudancin Somalia bayanda kasar Kenya ta rufe bakin iyakokinta domin hana su shiga cikin kasarta.

Jamian diplomasiya dai sunce gwamnatin Amurka ce ta baiwa dakarun Habasha dama da iznin shiga Somalia,tare da basu taimako na bayanai da kayan yaki.

Saboda gudun abinda ya faru ga dakarunta a a farkon 1990 a kasar ta Somalia,Amurkan bata fito ta nuna tana da hannu cikin wannan yaki ba,har sai jiya litinin.

Kasancewar sojojin Habasha da ake ganin kasa ce ta kirista ya janyo suka daga masu kishin kasa da kuma shugabanin addini a Somalia.

Sai dai duk da wannan suka shugaban kasar Somalia Abdullahi Yusuf wanda ya samu shiga Mogadishu karo na farko tun 2004 yace sojojin Habasah ba sun zo su mamaye Somalia bane,a cewarsa zasu fice daga kasar da zarar an samu kawnciyar hankali.

Haka shima shugaban Habashan Meles Zenawi cewa yayi yana son janye sojojinsa nan day a makonni kadan,amma kuma hakan ya dogara ne akan gaggauta aikewa da dakarun wanzar da zaman lafiya na Afrika da zasu maye gurbinsu.

 • Kwanan wata 09.01.2007
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btwj
 • Kwanan wata 09.01.2007
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btwj