Amurka ta ja kunnen Turkiya kan kai hari kan Qurdawa | Labarai | DW | 10.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta ja kunnen Turkiya kan kai hari kan Qurdawa

Kasar Amurka ta ja kunnen kasar Turkiyan game da tura sojojinta zuwa arewacin Iraki.Wata sanarwa daga maaikatar harkokin wajen kasar Amurka ta bukaci kasashen biyu da suyi aiki tare wajen magance wannan rikici.Tuni dai Firaminista Rajab Tayib Erdogan ya baiwa rundunar sojin kasar iznin daukar mataki kann yan tawaye na kungiyar PKK a Iraki.Cikin kwanaki uku da suka shige sojojin Turkiya uku suka halaka cikin hare hare na yan tawayen.Kasar Turkiyan tayi imanin cewa yan tawaye suna nan boye a yankin Qurdawa na kasar Irak inda suke samun makamai.A watan daya gabata ne kuma kasar Turkiyan ta sanya hannun tsakaninta da Amurka akan yarjejeniyar yaki da taadanci.Kasar Iraki kuma taki amincewa dakarun Turkiya shiga kasarta,saboda matsain lamba daga shugabanin lardin Qurdawa mai ikon cin gashin kansa.