Amurka ta gargadi Syria da Iran a game da.. | Labarai | DW | 27.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta gargadi Syria da Iran a game da..

Sakatariyyar harkokin wajen Amurka CR, ta gargadi Syria da Iran dasu shiga taitayin su na daina kawo cikas , a kokarin da ake na kawo karshen rikicin Israela da dakarun kungiyyar Hizbulla.

Rice wacce ta fadi hakan a kann hanyarta ta zuwa Malaysia, tace kin yin amfani da wannan gargadi ga kasashen biyu ka iya haifar da ci gaba da mayar dasu saniyar ware a harkoki na tsakanin kasa da kasa.

Kasar Amurka dai tuni ta goyi bayan matakin da Israela ta dauka na neman yan kungiyyar ta Hizbulla su janye daga iyakar kasar su da Lebanon kana a hannu daya kuma su kwance damara.

Rahotanni dai sun nunar da cewa, a yanzu haka tuni gamayyar kasa da kasa ta dukufa wajen ganin cewa an kawo karshen wannan rikici, da a yanzu haka yake kara neman jefa yankin na gabas ta tsakiya a cikin wani mawuyacin hali.