Amurka ta gargadi Koriya ta arewa | Labarai | DW | 20.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta gargadi Koriya ta arewa

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta gargadi Koriya ta arewa game da gwajin makami mai linzami mai dogon zango da tace zatayi.

Da take magana a birnin washington,Rice tace Amurka ba zata amince da wannan gwajin ba.

Kafofin yada labarai dai na Koriya ta kudu sun bada rahotannin cewa,babu makawa Koriya ta arewa tana shirin gwajin makamai masu linzami.

Kasashen Japan da New Zealanda da Australia suma sun baiyana damuwarsu dangane da yiwuwar wannan gwaji.

Ana ganin cewa makami mai linzami da Koriya ta arewan take shirin gwadawa,zai iya kaiwa kasar Amurka.

Shi dai jakadan kasar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya,John Bolton yace,Amurka tana nan tana tuntubar sauran kasashe membobin komitin sulhu domin daukar mataki akan Koriya ta arewa muddin dai ta ci gaba da wannan gwajin.