1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta bulo sa sabin hanyoyi na fusahar zamani wajen gano labarun asiri na jama'a--

Jamilu SaniJuly 15, 2004

Kungiyoyin kare hakin jama'a na duniya sun yi kakausan suka game da sabin hanyoyin da Amurka ta bulo da su ta neman labarun asiri na jama'a--

https://p.dw.com/p/Bvi6
Hoto: AP

A Shekara ta 1984 ne George Orwell wani dan asalin Amurka ya rubuta wani na labari game da yadda hukumomi zasu iya samun labaru na asirin halin rayuwa da jama’a ke ciki,to sai dai kuma a halin yanzu a iya cewa irin wadanan bayanai na shawarwari da dan asalin kasar ta Amurka ya rubuta a cikin litafin nasa sun fara baiyana a zahiri fiye da duk yadda mutane suke tunani.

A farkon wanan watan ne dai ga misali gidan talbijin din CNN ya bada wasu rahotani na yadda jami’an yan sandan Amurka suka fara amfani da wata karamar na’ura ta Computer da za’a iya sakawa a aljihu,wace kuma za’a iya amfani da ita wajen gano bayanai na asiri na dukan mutumin da ake zargin cewar mai laifi ne.

Wanan sabuwar hanya dai da Amurka ta bulo da ita ta sanin labarun asiri na jama’a na zaman wata sabuwar hanya ta fusahar zamani da Amurka ta bulo da ita wajen yaki da aiyukan tarzoma a duniya baki daya.

To sai dai kuma kungiyar kare hakin bil adama ta (ICLMG)ta Amurka dake da hadin kai wasu kungiyoyi masu zaman kann su da suka hadar dana Chochi Choci dana kare muhali da kare hakin jama’a sun yi kakausan suka game da sabin hanyoyi na fusahar zamani da Amurka ta bulo da ita ta neman labaru asiri na jama’a,inda suka ce yin zai shafi makomar yan gudun hijira dake zaune a Canada.

Kungiyoyin dai na kare hakin jama’a sun saka ayar tambaya kann yadda jami’an tsaron Amurka zasu iya bada bayanai asiri na gaskiya da jami’an tsaro da yan sandan Amurka zasu iya samu kann jama’a ko kuma bakin haure ta hanyar amfani da sabuwar fusahar zamani ta samun labarun asiri na jama’a ta la’akari da cewar ana iya samun kuskure wajen tattara irin wadanan bayanai.

A shekara ta 2002 ne dai jami’an tsaron Amurka suka kama wani dan asalin kasar Syria mai suna Maher Arar a filin saukar jiragen sama na New York bayan da suka zarge shi da kasancewa dan ta’ad,inda ba tare da wani bata lokaci ba suka tasa kiyarsa zuwa kasarsa ta haihuwa,bayan da aka shafe kusan shekara daya jami’an tsaron Amurka suna gana masa azaba ta fuskokin da dama.

Dan asalin kasar ta Syria injiniya a fanin harkar sadarwa mai shekaru 34 da haihuwa,ya bada labarin yadda jami’an tsaron Amurka suka rika gana masa azaba tare da tilasta masa bada bayanan da babu kanshin gaskiya a cikin su,a lokacin da jami’an tsaron Amurka ke yi masa tambayoyi bayan da aka zarge shi da laifin kasancewa dan ta’ada da kuma sabawa dokokin da suka shafi shige da ficen baki a cikin Amurka.