Amurka ta bawa mali tallafin dala million 461 | Labarai | DW | 13.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta bawa mali tallafin dala million 461

Amurka ta rattaba hannu akan yarjejeniyar tallafawa kasar Mali na kimanin dala million 461,wanda zaayi amfani dasu wajen gudanar da shirin noman rani da fadada filayen jiragen saman wannan kasa dake fama da talauci.Sakatariyyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice wadda tace tallafin na bangaren irin gudummowa da Amurka ke bawa kasashe ne,ta kuma bayyana cewa hakan na matsayin sakayya ne wa kyakkyawan shugabancin shugaba Amodou Toumani Toure na Malin.Rice tace akarkashin tsarin,Amurka na bada sakayya wa dukkan kasashe dasuke tafiyar da mulkin democradiyya cikin adalci da gaskiya.