Amurka ta bada umurnin cafke ko kashe jamian Irana dake Iraki | Labarai | DW | 26.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta bada umurnin cafke ko kashe jamian Irana dake Iraki

Shugaba Bush na Amurka ya baiwa dakarun Amurkan iznin su cafke ko kuma kashe jamian kasar Iran da suke cikin kasar Iraqi.

Jaridar Washington Times ta Amurkan ta ruwaito wani jamuin gwamnatin amurka dake da masaniya akan wannan shiri cewa Bush ya bada wannan umurnu ne tare da nufin rage karfin iko da Iran take da shi a yankin da kuma neman tilasta mata yin watsi da shirinta na nukiliya.

Jaridar tace wannan sabuwar manufa ta shafi jamian leken asiri ne na Iran da kuma jamian membobin rununar juyin juy hali na Iran da suke aiki tare da sojij sa kai,amma banda fafaren hula ko jamian diplomasiya.

Yanzu haka dai akwai yan Iran da dama da dakarun Amurka suka tsare a Iraq cikin watan daya gabata.

Jakadan Amurka mai barin gado a Iraqi zalmay Khalilzad yace nan bada jimawa ba zaa sanarwa jamaa irin zargi da ake tuhumar waddannan mutane da su.