Amurka ta aike da mazon ta izuwa Nigeria | Labarai | DW | 02.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta aike da mazon ta izuwa Nigeria

Amurka ta aike da manzonta izuwa birnin Abuja dake Nigeria don taimakawa wajen cimma sulhu a tsakanin wakilan kungiyoyin yan tawaye na Sudan da kuma bangaren gwamnati.

Daukar matakin aikewa da Mr Robert Zoellick dai izuwa tarayyar ta Nigeria yazo ne, bayan da aka fuskanci kiki kaka a game da tattaunawar sulhun dake wakana a birnin na Abuja a tsakanin bangarorin biyu.

Ya zuwa yanzu dai bayanai sun nunar da cewa tuni kungiyyar hadin kann kasashen Africa dake shiga tsakanin sasanta rikicin ta bawa bangarorin biyu wa´adi na awowi 24 dasu tantance banbance banbance su don amincewa da daftarin sulhun data gabatar.

Wannan dai daftari ya bukaci kwance damarar tsageru dake marawa gwamnatin kasar baya a hannu daya kuma da kungiyoyin yan tawayen dake rikici da gwamnati. Har ilya yau daftarin ya kuma bukaci shigar da yan tawayen a cikin rundunar soji ta kasar.